Luke 13

A Tuba ko a Hallaka

1A yanzun fa, akwai waɗansu da suka kasance a lokacin can, suka ba Yesu labarin Galiliyawa da Bilatus ya garwaya jininsu tare da jinin hadayunsu. 2Yesu ya amsa, ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galiliyawan sun fi dukan sauran Galiliyawa zunubi ne, shi ya sa suka sha irin wannan wahala? 3Ina gaya muku, aʼa! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka. 4Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya ya fāɗi a kansu a Silowam, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne? 5Ina gaya muku, aʼa! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.”

6Sai ya faɗa wannan misali, ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire ʼyaʼyan itacen, sai ya tarar ba ta yi ʼyaʼya ba. 7Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman ʼyaʼyan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’

8“ Mutumin ya amsa, ya ce, ‘Ranka yǎ daɗe, ka bar shi, in yi masa ban ƙasa, in kuma zuba masa taki har na shekara ɗaya. 9In kuwa ya ba da ʼyaʼya shekara mai zuwa, yana da kyau! In kuwa ba haka ba, sai ka sare shi.’ ”

Warkar da Gurguwa a Ranar Asabbaci.

10Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majamiʼa, 11a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan. 12Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an ʼyantar da ke daga rashin lafiyarki.” 13Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.

14Amma mai mulkin majamiʼar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.”

15Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba yakan kunce bijiminsa ko jakinsa, ya kai shi waje ya ba shi ruwa, a ranar Asabbaci ba? 16Ashe, ba ya kamata a ʼyantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya ɗaure ta ba?”

17Saʼad da ya faɗi wannan, sai duka masu gāba da shi suka kunyata. Amma mutane kuwa suka yi murna saboda dukan abubuwan banmamaki da yake yi.

Misalai na Ƙwayar Mustad da na Yisti

18Sai Yesu ya yi tambaya, ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi? 19Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa.”

20Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah? 21Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya garwaye ƙullun duka.”

Matsattsiyar Ƙofa

22Saʼad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa. 23Sai wani ya tambaye shi, ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?” Ya ce musu, 24“Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba. 25Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yǎ daɗe, buɗe mana ƙofa.’

“ Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’

26“ Saʼan nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’

27“ Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’

28“ Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, saʼad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje. 29Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah. 30Hakika, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.”

Baƙin Cikin Yesu Domin Urushalima

31A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.”

32Ya amma ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci, cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, saʼan nan a rana ta uku in cika burin aikina. 33Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, saʼan nan in ci gaba da yin haka washegari kuma, gama hakika, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’

34“ Ya, Urushalima, Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ʼyaʼyanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ʼyaʼyanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba! 35Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”

Copyright information for HauSRK